6 Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ku sassare itatuwanta,Ku tula ƙasa kewaye daUrushalima,Dole in hukunta wannan birnisaboda ba kome cikinsa saizalunci,
7 Kamar yadda rijiya take da ruwagarau,Haka Urushalima take damuguntarta,Ana jin labarin kama-karya da nahallakarwa a cikinta,Kullum akwai cuce-cuce, da raunukaa gabana,
8 Ku ji faɗaka, ya ku mutanenUrushalima,Don kada a raba ni da ku,Don kada in maishe ku kufai,Ƙasar da ba mazauna ciki.”
9 Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Za a kalace ringin Isra'ila sarai,kamar yadda ake wa inabi,Ka miƙa hannunka a kan rassantakamar mai tsinkar 'ya'yaninabi.”
10 Da wa zan yi magana don in faɗakarda shi, don su ji?Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, suji,Ga shi, maganar Ubangiji kuwa tazama abin ba'a a gare su,Ba su marmarinta.
11-12 Don haka ina cike da fushinUbangijiNa gaji da kannewa.Ubangiji ya ce,“Zan kwararo fushi kan yara da suke atiti.Da kuma kan tattaruwar samari.Za a ɗauke mata da miji duka biyu,Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufatukub-tukub.Za a ba waɗansu gidajensu, dagonakinsu, da matansu,Gama zan nuna ikona in hukuntamazaunan ƙasar.
13 Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,Kowannensu yana haɗama ya ciƙazamar riba,Har annabawa da firistoci,Kowannensu ya shiga aikata rashingaskiya.