16 “Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.
17 Ba ka ga abin da suke yi a biranen Yahuza da titunan Urushalima ba?
18 Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”
19 In ji Ubangiji, “Ni suke tsokana? Ashe, ba kansu ba ne don su ruɗar da kansu?”
20 Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”
21 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ku ba da hadayunku na ƙonawa da na sadakarku, ku ci naman.
22 A ranar da na fito da kakanninku daga ƙasar Masar, ban yi magana da su, ko na umarce su, a kan hadayun ƙonawa da na sadaka ba.