3 Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, ni kuwa zan ƙyale ku, ku zauna a wannan wuri.
4 Kada ku amince da maganganun nan na ruɗarwa, cewa wannan shi ne Haikalin Ubangiji. Wannan shi ne Haikalin Ubangiji, wannan shi ne Haikalin Ubangiji!
5 “ ‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku,
6 idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,
7 sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.
8 “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.
9 Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?