16 Daga Dan, an ji firjin dawakai.Dakan ƙasar ta girgiza sabodahaniniyar ingarmunsu.Sun zo su cinye ƙasar duk da abinda suke cikinta,Wato da birnin da mazaunacikinsa.”
17 “Ni Ubangiji na ce, ‘Zan aiko mukuda macizai, da kāsā,Waɗanda ba su da makari,Za su sassare ku.’ ”
18 Baƙin cikina ya fi ƙarfin warkewa,Zuciyata ta ɓaci ƙwarai!
19 Ku ji kukan jama'ata ko'ina aƙasar,“Ubangiji, ba shi a Sihiyonane?Sarkinta ba ya a cikinta ne?”Ubangiji ya ce,“Me ya sa suka tsokane ni dasassaƙaƙƙun gumakansu,Da baƙin gumakansu?”
20 Mutane suna ta cewa,“Damuna ta ƙare, kaka kuma tawuce,Amma ba a cece mu ba.”
21 Raunin da aka yi wa jama'ata,Ya yi wa zuciyata rauni.Ina makoki, tsoro kuma ya kama niƙwarai.
22 Ba abin sanyayawa a Gileyad ne?Ba mai magani a can ne?Me ya sa ba a warkar da jama'ataba?