2 Da ma ina da wurin da zan fake ahamada,Da sai in rabu da mutanena, in tafican!Gama dukansu mazinata ne,Ƙungiyar mutane maciya amana.
3 Ubangiji ya ce,“Sun tanƙwasa harshensu kamarbaka,Ƙarya ce take rinjayar gaskiya aƙasar.Suna ta cin gaba da aikata mugunta,Ba su kuwa san ni ba.
4 “Bari kowane mutum ya yi hankalida maƙwabcinsa,Kada kuma ya amince da kowaneirin ɗan'uwa,Gama kowane ɗan'uwa munafukine,Kowane maƙwabci kuma mai kushene.
5 Kowane mutum yana ruɗinmaƙwabcinsa da abokinsa,Ba mai faɗar gaskiya,Sun koya wa harshensu faɗarƙarya.Suna aikata laifi,Sun rafke, sun kasa tuba.
6 Suna ƙara zalunci a kan zalunci,Yaudara a kan yaudara,Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.
7 Saboda haka, Ubangiji MaiRunduna, ya faɗa cewa,“Zan tsabtace su, in gwada su,Gama me zan yi kuma sabodajama'ata?
8 Harshensu kibiya ce mai dafi, yanafaɗar ƙarya,Kowa yana maganar alheri damaƙwabcinsaAmma a zuciyarsa yana shirya masamaƙarƙashiya.