2 Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! 'Ya'yan da na goya sun tayar mini.
3 Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”
4 An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.
5 Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.
6 Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.
7 An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko'ina kufai.
8 Urushalima kaɗai ta ragu, birnin da aka kewaye da yaƙi, ba wata kariya kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, ko ta mai ƙumu a gonar kankana.