1 Wannan shi ne jawabi a kan Dimashƙu.Ubangiji ye ce, “Dimashƙu ba za ta ƙara zama birni ba, za ta zama tsibin kufai ne kawai.
2 Za a watse a bar biranen Suriya har abada. Za su zama makiyayar tumaki da shanu. Ba wanda zai tsoratar da su.
3 Ba za a kāre Isra'ila ba, Dimashƙu kuma za ta rasa 'yancinta. Suriyawan da suka ragu za su sha wulakanci kamar mutanen Isra'ila. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
4 Ubangiji ya ce, “Rana taba zuwa, ran da girman Isra'ila zai ƙāre, fatara za ta gāje gurbin dukiyarsu.
5 Isra'ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa'ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu.
6 Isra'ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe 'ya'yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”
7 A wannan rana, mutane za su juyo neman taimako ga Mahaliccinsu, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.