2 Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa.Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.
3 Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.
4 Kaina ya yi yum, ina ta rawar jiki saboda tsoro. Ina ta marmarin maraice ya yi, amma bai kawo mini kome ba, sai razana.
5 A wahayin na ga an shirya biki, an shisshimfiɗa darduma inda waɗanda aka gayyata za su zauna. Suna ci suna sha. Farat ɗaya sai aka ji umarni cewa, “Jarumawa! Ku shirya garkuwoyinku.”
6 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani.
7 Idan ya ga mutane biyu biyu suna zuwa a kan dawakai, waɗansu kuma a kan raƙuma da jakuna, ka faɗa masa ya lura da su sosai.”
8 Mai tsaro ya ce, “Ya mai girma, ina ta tsaro dare da rana a wurin da aka sa ni.”