6 Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani.
7 Idan ya ga mutane biyu biyu suna zuwa a kan dawakai, waɗansu kuma a kan raƙuma da jakuna, ka faɗa masa ya lura da su sosai.”
8 Mai tsaro ya ce, “Ya mai girma, ina ta tsaro dare da rana a wurin da aka sa ni.”
9 Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”
10 Ya jama'ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila.
11 Wannan shi ne jawabi a kan Edom.Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”
12 Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”