19 Ubangiji zai fisshe ka daga maƙaminka, ya ƙasƙantar da kai daga babban matsayinka!”
20 Ubangiji ya ce wa Shebna, “Idan haka ya faru zan aika wa bawana Eliyakim ɗan Hilkiya.
21 Zan sa masa tufafin sarautarka, in ɗaura masa ɗamara, in kuma ba shi dukan ikon da kake da shi. Zai zama kamar uba ga jama'ar Urushalima da na Yahuza.
22 Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.
23 Zan kafa shi da ƙarfi a wurin kamar turke, zai kuwa zama sanadin daraja ga dukan iyalinsa.
24 “Amma dukan 'yan'uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya!
25 Sa'ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”