15 Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.
16 Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.
17 Wata rana za ku ga sarki mai ɗaukaka yana mulki a dukan ƙasar da take shimfiɗe zuwa kowace kusurwa.
18 Tsoronku na dā game da baƙi masu tara haraji, magewaya, zai ƙare.
19 Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba!
20 Ku duba Sihiyona, birni inda muke idodinmu. Ku duba Urushalima! Za ta zama wurin zama mai lafiya! Za ta zama kamar alfarwar da ba ta taɓa gusawa ba, wadda ba a taɓa tumɓuke turakunta ba, igiyoyinta kuma ba su taɓa tsinkewa ba.
21 Ubangiji zai nuna mana ɗaukakarsa. Za mu zauna a gefen koguna da rafuffuka masu faɗi, amma ba kuwa jirgin ruwan abokan gāba da zai bi ta cikinsu.