6 Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!”Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?”“Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke,Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.
7 Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushiSa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu.Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!
8 Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi,Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”
9 Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima,Ki faɗi albishir!Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona,Ki faɗi albishir!Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro.Ki faɗa wa garuruwan Yahuza,Cewa Allahnsu yana zuwa!
10 Ubangiji yana zuwa ya yi mulki da iko,Zai taho tare da mutanen da ya cece su.Ga shi, zai kawo ladaZai kuma yi wa mutane sakamako.
11 Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi,Zai tattara 'yan raguna wuri ɗaya,Zai ɗauke su ya rungume su,A hankali zai bi da iyayensu.
12 Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu,Ko sararin sama da tafin hannunsa?Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali,Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?