18 Zan sa kogunan ruwa su yi gudu daga ƙeƙasassun tuddai,Maɓuɓɓugan ruwa su yi gudu a kwaruruka.Zan sa hamada ta zama kududdufan ruwa,Busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓuɓɓugan ruwa.
19 Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada,Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun.Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi,Jejin itatuwan fir.
20 Mutane za su ga wannan, su sani,Ni Ubangiji, na yi shi.Za su fahimta,Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya sa abin ya faru.”
21 Ubangiji, Sarki na Isra'ila, ya faɗi wannan,“Ku allolin al'ummai ku gabatar da matsalarku.Ku kawo dukan gardandamin da kuke da su!
22 Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba,Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru,Ku faɗa mana yadda zai zama duka,Domin lokacin da ya faru mu mu sani.
23 Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa.Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne!Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i,Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!
24 Ku da dukan abin da kuke yi ba kome ba ne,Waɗanda suke yi muku sujada kuwa,Abin ƙyama ne su!