13 Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.
14 Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma.
15 Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada!
16 Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”
17 Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”
18 Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.
19 Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”