15 Mutum yakan yi abin wuta da wani sashi na itacen, wani sashi kuma ya yi gunki da shi. Yakan hura wuta da wani sashi don ya ji ɗumi, yakan kuma toya gurasa. Yakan yi gunki da wani sashi, ya riƙa yi masa sujada!
16 Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”
17 Sauran itacen ya mai da shi gunki. Yana rusunawa ya yi masa sujada. Yana addu'a gare shi yana cewa, “Kai ne Allahna, ka cece ni!”
18 Irin waɗannan mutane dakikai ne, har ba su san abin da suke yi ba. Sun rufe idanunsu da tunaninsu ga gaskiya.
19 Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”
20 Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.
21 Ubangiji ya ce,“Ka tuna da waɗannan abu, ya Isra'ila,Ka tuna kai bawana ne.Na halicce ka domin ka zama bawana,Ba zan taɓa mantawa da kai ba.