4 Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra'ila,Jama'ar da ni na zaɓa.Na ba ka girma mai yawa,Ko da yake kai ba ka san ni ba.
5 “Ni ne Ubangiji, ba wani Allah sai ni.Zan ba ka irin ƙarfin da kake bukata,Ko da yake kai ba ka san ni ba.
6 Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancanSu sani ni ne Ubangiji,Ba kuwa wani Allah sai ni.
7 Ni na halicci haske duk da duhu,Ni ne na kawo albarka duk da la'ana.Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.
8 Zan aiko da nasara daga sararin sama kamar ruwan sama.Ƙasa za ta buɗe ta karɓe ta,Za ta kuwa hudo da 'yanci da gaskiya.Ni Ubangiji, ni zan sa haka ya faru.”
9 Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta,Tukunyar da take daidai da sauran tukwane?Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi?Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta?
10 Ko akwai wanda zai iya ce wa iyayensa,“Don me kuka haife ni kamar haka?”