3 “Ku kasa kunne gare ni ku zuriyar Yakubu,Dukanku, mutanena da kuka ragu.Ina ta lura da ku tun daga lokacin da aka haife ku.
4 Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
5 Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?Akwai wani mai kama da ni?
6 Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,Suna auna azurfa a kan ma'auni.Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!
7 Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi,Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can,Ba ya iya motsawa daga inda yake.Idan wani ya yi addu'a gare shi, ba zai iya amsawa ba,Ko ya cece shi daga bala'i.
8 “Ku tuna da wannan, ku masu zunubi,Ku dubi irin abin da na yi.
9 Ku tuna da abin da ya faru tuntuni,Ku sani, ni kaɗai ne Allah,Ba kuwa wani mai kama da ni.