4 Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku,Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura.Ni na halice ku zan kuwa lura da ku,Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
5 Ubangiji ya ce, “Da wane ne za ku kwatanta ni?Akwai wani mai kama da ni?
6 Mutane suka buɗe alabensu suna zazzage zinariya,Suna auna azurfa a kan ma'auni.Suka yi jingar maƙerin zinariya don ya yi musu gunki,Sa'an nan suka rusuna suka yi masa sujada!
7 Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi,Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can,Ba ya iya motsawa daga inda yake.Idan wani ya yi addu'a gare shi, ba zai iya amsawa ba,Ko ya cece shi daga bala'i.
8 “Ku tuna da wannan, ku masu zunubi,Ku dubi irin abin da na yi.
9 Ku tuna da abin da ya faru tuntuni,Ku sani, ni kaɗai ne Allah,Ba kuwa wani mai kama da ni.
10 Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama,Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru.Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba,Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.