2 Ki fāɗaɗa alfarwar da kike zama ciki!Ki ƙara tsawon igiyoyinta, ki kuma ƙara ƙarfin turakunta!
3 Za ki faɗaɗa kan iyakar ƙasarki a kowane gefe,Jama'arki za su karɓi ƙasarsuWadda al'ummai suke mallaka yanzu,Biranen da aka bari ba kowa, za su cika da mutane.
4 Kada ki ji tsoro, ba za a ƙara kunyatar da ke ba,Ba kuwa za a ƙasƙantar da ke ba.Za ki manta da rashin amincinki irin na matar ƙuruciya,Za ki manta da matsanancin kaɗaicinki,Mai kama da na gwauruwa.
5 Mahaliccinki zai zama kamar miji a gare ki,Sunansa Ubangiji Mai Runduna!Allah Mai Tsarki na Isra'ila mai fansarki ne,Shi ne mai mulkin dukan duniya!
6 Kina kama da amaryaWadda mijinta ya rabu da ita, tana baƙin ciki ƙwarai.Amma Ubangiji yana kiranki zuwa gare shi, ya ce,
7 “A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke,Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.
8 Na juya, na rabu da ke da fushi na ɗan lokaci,Amma zan nuna miki ƙaunata har abada.”Haka Ubangiji mai fansarki ya faɗa, shi wanda ya cece ki.