10 Muna ta lalubar bango kamar makafi, muna ta lalubawa kamar marasa idanu. Da tsakar rana muke ta tuntuɓe, sai ka ce da almuru. A tsakanin waɗanda suke da cikakken ƙarfi, kamar matattu muke.
11 Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.
12 “Gama laifofinmu sun yi yawa a gabanka, zunubanmu kuwa suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu suna tare da mu, muna kuwa sane da laifofinmu,
13 wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.
14 Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba.
15 Gaskiya ba ta, wanda ba ya aikata mugunta ya zama ganima.”Ubangiji ya gani, bai kuwa ji daɗi ba, da yake gaskiya ba ta.
16 Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa'an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa.