3 Domin in kawo wa masu makoki a SihiyonaFarin ciki da murna maimakon baƙin ciki,Waƙar yabo maimakon ɓacin rai.Ubangiji kansa zai lura da su,Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa.Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai,Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.
4 Za su sāke gina biranen da suke a rurrushe tun da daɗewa.
5 Ya Urushalima, baƙi za su bauta miki,Za su lura da garkunanki,Za su nome gonakinki, su gyara gonakinki na inabi.
6 Amma za a sani, ku firistoci ne na Ubangiji,Za ku mori dukiyar al'ummai,Za ku yi fāriya da cewa, taku ce.
7 Kunyarku da shan wulakancinku za su ƙare.Za ku zauna a ƙasarku,Za a riɓanya dukiyarku,Za ku yi ta farin ciki har abada.
8 Ubangiji ya ce,“Ina ƙaunar aikin gaskiya,Amma ina ƙin zalunci da aikata laifi.Da aminci zan ba mutanena lada,In yi madawwamin alkawari, da su.
9 Za su yi suna a cikin al'ummai,Dukan wanda ya gan su zai sani,Su ne mutanen da na sa wa albarka.”