1 Waɗannan su ne sarakunan ƙasar, waɗanda Isra'ilawa suka cinye da yaƙi, suka mallaki ƙasarsu a hayin Kogin Urdun daga yamma, tun daga kwarin Arnon har zuwa Dutsen Harmon da dukan Araba a wajen gabas,
2 Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda yake zaune a Heshbon, wanda yake mulki tun daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa Kogin Yabbok a iyakar Ammonawa,
3 daga kuma Araba zuwa gabashin Tekun Kinneret da zuwa Tekun Araga, wato Tekun Gishiri, a wajen gabas ta hanyar Ber-yeshimot, da wajen kudu zuwa gangaren gindin Dutsen Fisga,
4 da kuma Og, Sarkin Bashan, ɗaya daga cikin sauran Refayawa, wato gwarzayen nan waɗanda suka zauna a Ashtarot da Edirai.
5 Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.
6 Sai Musa, bawan Ubangiji, da Isra'ilawa suka ci sarakunan nan da yaƙi, sa'an nan ya ba da ƙasarsu ga Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa.