1 Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.
2 Har yanzu akwai sauran kabila bakwai na Isra'ila waɗanda ba su sami gādonsu ba tukuna.
3 Sai Joshuwa ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku ya ba ku?
4 Ku ba ni mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su auna ƙasar yadda za a raba ta gādo, sa'an nan su komo wurina.