3 Sai Joshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa mutanen kaciya a Gibeyat-ha'aralot, wato dutsen kaciya.
4-5 Dalilin da ya sa Joshuwa ya yi musu kaciya ke nan, domin dukan waɗanda aka haifa a hanya cikin jeji bayan fitowarsu daga Masar, ba a yi musu kaciya ba. Dukan mazajen da suka fito daga Masar waɗanda suka isa yaƙi sun rasu cikin jeji a hanyarsu. Waɗannan kuwa an yi musu kaciya kafin fitowarsu.
6 Gama shekara arba'in Isra'ilawa suna ta tafiya a jeji, har dukan al'umma, har da mayaƙan da suka fito daga Masar, suka hallaka, domin ba su kula da muryar Ubangiji ba. A gare su kuwa Ubangiji ya rantse, ba zai bar su su ga ƙasar da ya rantse wa kakanninsu zai ba su ba, ƙasar da take mai yalwar abinci.
7 'Ya'yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba.
8 Da aka gama yi wa al'ummar duka kaciya, sai suka zauna a zango har suka warke.
9 Sai Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “A wannan rana na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka, har wa yau ake kiran sunan wurin Gilgal, wato a kawar.
10 Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.