15 Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na 'ya'yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
16 Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele'azara da Itamar, 'ya'yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce,
17 “Don me ba ku ci hadaya don zunubi a wuri mai tsarki ba, da yake tsattsarkan abu ne wanda aka ba ku domin ku kawar da laifin taron jama'a, domin kuma ku yi kafara dominsu a gaban Ubangiji?
18 Ga shi, ba a shigar da jinin can cikin Wuri Mai Tsarki ba. Ga shi kuwa, ya kamata ku ci kamar yadda na umarta amma ba ku yi ba.”
19 Sai Haruna ya ce wa Musa, “Ga shi, yau suka miƙa hadayarsu don zunubi, da ta ƙonawa a gaban Ubangiji, ga kuma irin waɗannan abubuwa da suka same ni, da a ce na ci hadaya don zunubi yau, da zai yi kyau ke nan a gaban Ubangiji?”
20 Da Musa ya ji wannan, sai ya yi na'am da shi.