9 “Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.
10 “Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar.
11 Mutumin kuma da ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa ke nan, su biyu ɗin za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.
12 Duk wanda ya kwana da matar ɗansa, za a kashe su duka biyu ɗin, gama sun yi abin da yake haram. Alhakin jininsu yana wuyansu.
13 Duk mutumin da ya kwana da namiji kamar yadda namiji yake kwana da mace, su biyu ɗin, sun yi aikin ƙazanta, za a kashe su. Alhakin jininsu yana wuyansu.
14 Duk mutumin da ya auri 'ya tare da mahaifiyarta, wannan mugun abu ne, shi da su biyu ɗin, sai a ƙone su da wuta, don kada mugun abu ya kasance a cikinku.
15 Idan mutum ya kwana da dabba, sai a kashe shi, a kuma kashe dabbar.