19 Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu.
20 Kada ku yi hadaya da abin da yake da lahani, gama Ubangiji ba zai karɓa ba.
21 Idan kuwa wani ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji don cika wa'adi, ko don hadaya ta yardar rai, daga cikin garken shanu, ko na tumaki, da na awaki, sai ya zama cikakke, marar lahani, don ya karɓu.
22 Dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko mai gundumi, ko mai ɗiga, ko mai susa, ko mai kirci, kada ku miƙa wa Ubangiji, kada kuma ku yi hadaya ta ƙonawa a bagaden Ubangiji da su.
23 Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba.
24 Kowace dabba kuma da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa, ba za ku miƙa ta hadaya ga Ubangiji ba, ba kuwa za ku yi hadaya da ita a ƙasarku ba.
25 “Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.”