27 In wani daga cikin talakawa ya yi zunubi, ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.
28 Sa'ad da aka sanar da shi zunubin da ya aikata, sai ya kawo akuya marar lahani don yin hadaya saboda zunubinsa.
29 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa.
30 Firist zai ɗibi jinin da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden.
31 Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
32 Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani.
33 Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.