30 Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”
31 Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”
32 Haka suka kawo wa 'yan'uwansu, Isra'ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne.
33 Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”