33 'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin.
34 Bisa ga kwanakin nan arba'in da kuka leƙi asirin ƙasar, haka za ku ɗauki alhakin zunubanku shekara arba'in, gama kowane kwana a maimakon shekara yake. Ta haka za ku sani ban ji daɗin abin da kuka yi ba.
35 Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama'ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”
36 Mutanen da Musa ya aika su leƙo asirin ƙasar, waɗanda suka komo, suka sa taron jama'a su yi gunaguni a kansa saboda sun kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar,
37 mutanen nan da suka kawo rahoto mai banrazana a kan ƙasar, annoba ta kashe su a gaban Ubangiji.
38 Sai dai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne, kaɗai ne ba za su mutu ba daga cikin waɗanda suka tafi leƙen asirin ƙasar.
39 Da Musa ya faɗa wa Isra'ilawa abin da Ubangiji ya ce, sai jama'a suka yi baƙin ciki ƙwarai.