7 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da sulusin moɗa na ruwan inabi, don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
8 Idan kuwa da bijimi ne za a yi hadaya ta ƙonawar, ko sadaka domin cika wa'adi, ko ta salama ga Ubangiji,
9 sai a miƙa hadaya ta gari tare da bijimin, humushi uku na garwar gari kwaɓaɓɓe da rabin moɗa na mai.
10 Za a kuma miƙa hadaya ta sha da rabin moɗa na ruwan inabi. Hadaya ce da akan yi da wuta, mai yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
11 Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago,ko ɗan rago,ko bunsuru.
12 Bisa ga yawan abin da aka shirya, haka za a yi da kowannensu bisa ga adadinsu.
13 Haka dukan waɗanda suke 'yan ƙasa za su yi in za su ba da hadayar da akan yi da wuta don yin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.