14 “Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra'ila zai zama naka.
15 “Dukan haihuwar fari, ko ta mutum ko ta dabba da sukan bayar ga Ubangiji zai zama naka. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.
16 Sai ka fanshe su suna 'yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
17 Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.
18 Naman kuwa zai zama naka, duk da ƙirji na kaɗawa da cinyar dama da aka miƙa su hadaya ta kaɗawa.
19 “Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra'ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da 'ya'yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”
20 Ubangiji kuma ya ce wa Haruna, “Ba za ka gāji kome a ƙasar Isra'ilawa ba, ba ka da wani rabo a cikinta. Ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra'ilawa.”