25-31 Ƙungiyoyin kabilar Dan za su sauka su kafa tutarsu a sashin arewa a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai 62,700 Ashiru Fagiyel ɗan Okran 41,500 Naftali Ahira ɗan Enan 53,400 Jimilla duka, (157,600) duba ɗari da hamsin da bakwai, da ɗari shida.Ƙungiyoyin Dan za su bi daga bayan duka.
32 Jimillar yawan Isra'ilawa da aka rubuta su a yadda suke ƙungiya ƙungiya, su dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin ne (603,550).
33 Amma kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ba a rubuta Lawiyawa haɗe da sauran Isra'ilawa ba.
34 Saboda haka Isra'ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.