1 Da Sarkin Arad, Bakan'ane, wanda yake zaune a Negeb, ya ji Isra'ilawa suna zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fita ya yi yaƙi da Isra'ilawa, ya kama waɗansu daga cikinsu.
2 Sai Isra'ilawa suka yi wa'adi ga Ubangiji, suka ce, “In hakika, za ka ba da mutanen nan a hannunmu, lalle za mu hallaka biranensu ƙaƙaf.”
3 Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.
4 Isra'ilawa suka kama hanya daga Dutsen Hor zuwa Bahar Maliya don su kauce wa ƙasar Edom. Sai jama'a suka ƙosa da hanyar.