5 Suka yi wa Allah gunaguni, da Musa kuma, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu cikin jeji mu mutu? Gama ba abinci, ba ruwa, mu kuwa mun gundura da wannan abinci marar amfani.”
6 Sai Ubangiji ya aiko macizai masu zafin dafi a cikin jama'a, suka sassari Isra'ilawa, da yawa kuwa suka mutu.
7 Jama'a kuwa suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi gama mun yi wa Ubangiji gunaguni, mun kuma yi maka. Ka roƙi Ubangiji ya kawar mana da macizan.” Musa kuwa ya yi roƙo domin jama'ar.
8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera maciji da tagulla, ka sarƙafa shi a bisa dirka, duk wanda maciji ya sare shi, idan ya dubi maciji na tagullar, zai rayu.”
9 Musa kuwa ya yi maciji na tagulla, ya sarƙafa shi a bisa dirka, idan kuwa maciji ya sari mutum, in ya dubi macijin tagullar, zai warke.
10 Sai mutanen Isra'ila suka kama hanya, suka yi zango a Obot.
11 Suka kama hanya daga Obot, suka yi zango a kufafen Abarim a cikin jeji daura da Mowab wajen gabas.