1 Da Bal'amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra'ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji,
2 ya ta da idanunsa ya ga Isra'ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa.
3 Sai ya yi annabcinsa, ya ce.“Faɗar Bal'amu ɗan Beyor,Faɗar mutumin da idonsa take a buɗe.
4 Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki,Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.
5 Alfarwan Isra'ilawa suna da kyan gani!
6 Kamar dogon jerin itatuwan dabino,Kamar gonaki a gefen kogi,Kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,Kamar kuma itatuwan al'ul a gefen ruwaye.