15 Sunan Bamadayaniya kuwa, Kozbi, 'yar Zur. Shi ne shugaban mutanen gidan ubansa a Madayana.
16 Ubangiji kuma ya umarci Musa, ya ce,
17 “Ku fāɗa wa Madayanawa ku hallaka su.
18 Gama sun dame ku da makircinsu da suka yaudare ku a kan al'amarin Feyor da na Kozbi 'yar'uwarsu, 'yar shugaban Madayana, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor.”