38 Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram,
39 da Shuffim, da Huffim.
40 Iyalin Adar da na Na'aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne.
41 Waɗannan su ne 'ya'yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari shida (45,600).
42 Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan.
43 Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).
44 Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya.