15 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.
16 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
17 A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani.
18 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
19 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gari, da hadayarsu ta sha.
20 A rana ta uku ta idin za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
21 Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.