27 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
28 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
29 A rana ta shida ta idin za a miƙa bijimai takwas, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
30 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
31 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya taƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
32 A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
33 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.