5 Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara.
6 Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
7 Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba.
8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi ɗaya, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.
9 Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon,
10 da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.
11 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.