13 Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”
14 Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sinai, ya ce masa
15 ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba.
16 Haka Musa ya ƙidaya su bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda ya umarce shi.
17 Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari.
18 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai.
19 Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.