42 Sai Musa ya ƙidaya 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
43 Jimillar 'ya'yan fari maza da aka ƙidaya bisa ga sunayensu tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu ashirin da biyu, da ɗari biyu da saba'in da uku ne (22,273).
44 Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce,
45 “Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.
46 'Ya'yan fari maza na Isra'ilawa sun fi Lawiyawa da mutum ɗari biyu da saba'in da uku. Sai a fanshi wannan ragowa.
47 Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
48 Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da 'ya'yansa maza.”