3 Idan kuma mace ta yi wa'adi ga Ubangiji, ta kuma ɗaure kanta da rantsuwa tun tana yarinya a gidan mahaifinta,
4 idan mahaifinta ya ji wa'adinta da rantsuwarta wadda ta ɗaure kanta da su, bai ce mata kome ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.
5 Amma idan mahaifinta ya ji, ya nuna rashin yarda, to, wa'adinta da rantsuwarta ba za su tsaya ba, Ubangiji kuwa zai gafarce ta domin mahaifinta bai yardar mata ba.
6 Idan kuwa ta yi aure lokacin da take da wa'adi ko kuwa rantsuwar da ta yi da garaje,
7 idan mijinta ya ji wa'adin ko rantsuwar amma bai ce mata kome ba a ranar da ya ji, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su tabbata.
8 Amma idan mijinta bai goyi bayanta a ranar da ya ji ba, to, sai wa'adinta da rantsuwarta su warware, Ubangiji kuwa zai gafarce ta.
9 Mace wadda mijinta ya rasu ko sakakkiya, dole ta cika wa'adin da ta yi, da kowane alkawari, za su tabbata.