1 Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Ka ɗaukar wa Isra'ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”
3 Musa kuwa ya ce wa jama'a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu.
4 Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila zuwa wurin yaƙi.”
5 Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra'ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.