45 jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500),
46 'yan mata dubu goma sha shida (16,000).
47 Daga rabin kashi na jama'ar Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na 'yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
48 Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa.
49 Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu.
50 Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da 'yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
51 Musa da Ele'azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka.