1 Kabilan Ra'ubainu da Gad suna da dabbobi da yawa ƙwarai. Da suka ga ƙasar Yazar da ta Gileyad wuri ne mai kyau domin shanu,
2 sai suka je wurin Musa da Ele'azara firist, da shugabannin taron jama'ar,
3 suka ce, “Atarot, da Dibon, da Yazar, da Bet-nimra, da Heshbon, da Eleyale, da Simba, da Nebo, da Ba'al-meyon,
4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama'a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa.
5 Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”
6 Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai 'yan'uwanku su yi ta yaƙi,ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko?