5 Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”
6 Amma Musa ya amsa musu ya ce, “Wato sai 'yan'uwanku su yi ta yaƙi,ku kuwa ku yi zamanku a nan, ko?
7 Don me za ku karya zuciyar jama'ar Isra'ila daga hayewa zuwa ƙasar da Ubangiji ya ba su?
8 Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.
9 Gama sa'ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama'a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
10 Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa'adi ya ce,
11 ‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba.