9 Gama sa'ad da suka tafi Kwarin Eshkol suka ga ƙasar, suka karya zuciyar jama'a daga shigar ƙasar da Ubangiji ya ba su.
10 Saboda haka Ubangiji ya husata a ranan nan, har ya yi wa'adi ya ce,
11 ‘Hakika ba wani daga cikin mutanen da suka fito daga Masar, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba da zai ga ƙasar da na rantse zan ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, domin ba su bi ni sosai ba.
12 Sai dai Kalibu, ɗan Yefunne Bakenizze, da Joshuwa ɗan Nun, domin su ne kaɗai suka bi ni sosai.’
13 Saboda Ubangiji ya husata da isra'ilawa, shi ya sa suka yi ta yawo a jeji har shekara arba'in, wato sai da tsaran nan wadda ta aikata mugunta a gaban Ubangiji ta ƙare.
14 Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
15 Gama idan kun ƙi binsa, zai sāke yashe ku a jeji. Ku ne kuwa za ku zama sanadin hallakar mutanen nan duka.”