1 A filayen Mowab a wajen Urdun daura da Yariko, Ubangiji ya yi magana da Musa, ya ce,
2 “Ka umarci jama'ar Isra'ila, ka ce su ba Lawiyawa biranen da za su zauna a ciki daga cikin gādonsu, za su kuma ba Lawiyawa hurumi kewaye da biranen.
3 Biranen za su zama nasu, inda za su zauna, hurumi kuwa domin shanunsu da sauran dukan dabbobinsu.
4 Girman hurumin da za su ba Lawiyawa kewaye da biranen zai zama mai fāɗin kamu dubu kewaye da garun birnin.
5 A bayan birnin za a auna kamu dubu biyu a wajen gabas, kamu dubu biyu a wajen kudu, kamu dubu biyu a wajen yamma, kamu dubu biyu a wajen arewa. Wannan zai zama hurumin mutanen birnin. Birnin kuwa zai kasance a tsakiya.